Alhaji Dahiru Abubakar Kibiya, mai shekaru 38 daga jihar Kano na daya daga cikin mahajjatan da su ka tafi kasar Saudiyya aikin hajjin bana.
A karshe da ya dawo gida bayan ya shafe kwanaki 35 a sashin kula da lafiya na wani asibiti da ke Madina, Saudi Arebiya.
Binciken jaridar Blueprint ya nuna cewa, Dahiru bai samu damar gudanar da ibadar aikin hajjin da aka saba ba, saboda ya kamu da wata cuta a huhunsa, wanda daga karshe ya tilasta masa l kwanciya a asibitin a duk tsawon lokacin aikin hajjin.
Da yake bayyana irin halin da ya shiga a shelkwatar Hukumar Alhazai ta jihar Kano a jiya Alhamis, Dahiru ya ce warke wa daga irin wannan muguwar jarabar na bukatar godiya ga mahaliccinsa da ya ba shi damar tsira.
Ya ce bai taba tunanin zai warke daga cutar ba bayan an samu nasarar gano ciwon.
Ya ce an magance ciwon sakamakon kulawa mai karfi daga hukumar asibitin da kuma kulawa sosai daga jami’an hukumar alhazai ta jiha da kuma hukumomin lafiya a asibitin a tsawon zamansa.
Ya kara da cewa a cikin irin wannan mawuyacin hali, mutum na bukatar kulawa cikin gaggawa.