Kafofin yaɗa labarai da dama daga Ƙasar Saudiyya sun rawaito cewa, ƙasar ta bai wa alhazan Ummarah damar zama ƙasar zuwa tsawon kwana 90 idan sun so.
Kazalika, alhazan na da zaɓin yin amfani da kowane filin jirgin saman da suka yi ra’ayi a ƙasar.
Saboda a cewar Ma’aikatar Hajji da Ummarah ta Saudiyya, ba a ƙayyade wa alhazan filayen jiragen saman da za su yi mu’amala da su a faɗin ƙasar ba, walau manyan filayen jiragen sama ko ƙanana.
Haka nan, Ma’aikatar ta ce alhazan na da damar ci gaba da zama a masarautar har na tsawon kwana 90, sannan suna da damar yin zirga-zirga tsakanin Makka da Madina da kuma sauran birane a faɗin masarautar.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa, maniyyata na iya neman bisa ta hanyar amfani da kafofin da aka samar don buƙatar hakan.
Sai dai, Ma’aikatar ta ce wajibi ne ga masu bisar Ummarah su yi amfani da manhajar Eatmarna don tabbatar da ba su ɗauke da cutar Korona, ko kuma an yi mu’amala da wani mai ɗauke da cutar.