Hukumar Kula da Walwalar Alhazai ta Birnin Tarayya Abuja, ta ce a shirye take da ta ci gaba da hulɗa da kafar IHR a fannin harkokin Hajji Umarah.
Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata wasiƙar godiya da jinjina da ta aike wa IHR a ranar Talatar da ta gabata ta hannun Daraktan Hukumar, Malam Muhammad Nasiru DanMallam,
Hukumar ta yi wannan yabo ne biyo bayan lambar yabo guda biyu da ta samu kan kyautata ayyukan Hajjin 2022 daga IHR yayin tron lakca da miƙa lambobin yabo ga waɗanda suka cancanta wanda IHR ɗin ta shirya a makon jiya.
Taron lakcar ya gudana ne a babban zauren taro na Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
A cewar DanMallam lambobin yabon da IHR ta bai wa hukumar tasu hakan zai ƙarfafa musu ƙara jajircewa wajen gudanar da ayyukan Hajji a gaba.
Daga nan, DanMallam ya ce ƙoƙari da kuma gudunmawar da IHR ke bayarwa a fagen Hajji da Umara a Nijeriya, abin a yaba ne