NAHCON ta kafa kwamitocin ƙaddamar wa Cibiyar Horon Aikin Hajji

0
349

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Zikrullah Kunke Hassan, ya ƙaddamar da wasu kwamitoci masu muhimmanci guda biyu waɗanda za su kula da sha’anin ƙaddamar da Cibiyar Horon Aikin Hajji ta Ƙasa.

A jiya Juma’a, 30 ga Satumba, 2022, a ka kafa kwamitocin a birnin tarayya, Abuja.

Cibiyar ita ce irin ta ta farko a yankin Afrika ta Yamma, wacce ke buƙatar a wakilta ƙwararru wajen gudanar da ita don cimma manufar kafa ta.

Kwamitin shirya taron wayar da kai da kuma da buɗe cibiyar zai gudana ne ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Tsare-Tsare da Kula da Ma’aikata da Sha’anin Kuɗi (PPMF), Alhaji Nura Yakasai, yayin da Alhaji Dikko Ibrahim Yar’adua zai jagoranci kwamitin sanya ido kan yadda ayyukan za su gudana.

Da ya ke jawabi yayin ƙaddamar da kwamitocin, Zikrullah ya ce yana da yaƙini gami da ƙwarin gwiwar mamabobin kwamitin za su sauke nauyin da aka ɗora musu yadda ya dace.

Kana ya yi kira ga ‘yan kwamitin da su maida hankali su yi aiki bil haƙƙi tare da jajircewa ta yadda a ƙarshe za su yi nasarar sauke nauyin da ya rataya a kansu.

Alhaji Yakasai ya nuna yabawarsu ga hukumar bisa wakilta su da aka yi don aiwatar da wannan aiki, tare da ba da tabbacin za su yi bakin ƙoƙarinsu wajen yin abin da ya kamata.