Hajjin baɗi: Hukumar alhazai ta Kaduna ta kafa kwamitin yi wa manhajar bita garambawul

0
416

A matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen Hajjin 2023, Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna ta kafa wani kwamitin musamman da zai waiwayi manhajar shirye-shiryen bita ga maniyyata a jihar.

Sakataren hukumar, Dakta Yusuf Yakubu Arrigasiyu ne ya ƙaddamar da kwamitin a ranar Talata a zauren taro na Otel din Asa Pyramid da ke Kaduna.

Mambobi 12 da kwamitin ya ƙunsa, an zaɓo su ne a tsakanin malamai da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa-da-tsaki a harkokin Hajji.

Da ya ke jawabi yayin ƙaddamarwar, Dr Arrigasiyu ya yi alƙawarin bai wa kwamitin dukkan gudunmawar da ya ke buƙata wajen sauke nauyin da aka ɗora masa.

Kwamitin zai gudana ne ƙarƙashin jagorancin Dakta Hadiza Ahmad Tukur daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, da sauran fitattun malaman Islama irin su Imam Tukur Al Manar a matsayin mambobi.