Sabon Shugaban Hukumar Alhazai na Jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri, ya kama aiki bayan da shugaba mai barin gado, Alhaji Bukar Kime Dapsa ya kammala wa’adinsa na shekara huɗu.
A ranar Labara aka miƙa wa sabon shugaban ragamar aiki a babban zauren taron hukumar a Damaturu, babban birnin jihar.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaba mai barin gado, Alhaji Bukar kime Dapsa ya yaba wa gwamnatin jihar bisa damar da ta ba shi na yi wa jihar hidima ta hukumar alhazan jihar.
Alhaji Bukar ya nuna godiyarsa ga Gwamna Mai Mala Buni da hukumar gudanarwa gami da ilahirin ma’aikatan hukumar dangane da irin haɗin kai da goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake riƙe da hukumar.
Daga nan ya yi kira ga ma’aikatan hukumar da su bai wa sabon shugaban haɗin kan da ya dace tare kuma da maida hankali a kan aikinsu.
A nasa jawabin, sabon Shugaban Hukumar, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri, ya buƙaci ma’aikatan hukumar su ba shi goyon bayan da ya dace don a gudu tare, a tsira tare.
Haka nan, ya yi godiya ga shugaba mai barin gado da ɗaukacin ma’aikatan hukumar bisa kyakkyawar tarbar da suka yi masa sa’ilin da ya shigo don kama aiki.
HAJJ REPORTERS ta rawaito cewa, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya naɗa Alhaji Mai Usman Biriri a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar alhazai na jihar.
Sakataren Gwamnatin jihar, Baba Malam Wali ne ya sanar da naɗin cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 23 ga Satumba, 2022, da kuma lamba: GO/S/EST/62/S.2.
Kodayake wasiƙar ta ce naɗin na riƙon ƙwarya ne, amma Sakataren ya ce naɗin na wa’adin farko na shekaru huɗu masu zuwa wanda ya fara aiki daga ran 6 ga Oktoba, 2022.
Wasiƙar ta nuna an bai wa Biriri sabon muƙamin ne duba da gudunmawar da ya bayar ga cigaban jihar. Tare da fatan zai ci gaba da kyawawan ayyukansa don amfanin jihar da al’umarta baki ɗaya.
Bayanai sun nuna cewa, a ƙarƙashin shugaba mai barin gado hukumar alhazan jihar ta samu tarin nasarori wanda hakan ya kai hukumar ga samun lambar yabo dangane da ayyukan Hajjin 2022 daga hukumar NAHCON da kuma IHR.