Allah Ya yi wa Sheikh Usman Saleh Rasuwa

0
295

Allah Ya yi wa fitaccen malamin nan na Kaduna, Sheikh Usman Saleh, rasuwa ran Juma’a.

Kafin rasuwarsa, marigayi Sheikh Usman Saleh ya kasance ɗaya daga cikin malaman da ke faɗakarwa da kuma ilimantar da maniyyata.

Kuma mamba ne a kwamitin wayar da kan maniyyata ƙarƙashin Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna na shekaru da dama.

Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna ce ta bayar da sanarwar rasuwar marigayin a ranar Juma’a ta zaurenta na WhatsApp.

Sanarwar ta nuna za a yi jana’izar marigayin ne a Masallacin ‘yan Lilo da ke Tudun Wadan, Kaduna da zarar an sauka Juma’a.

Da fatan Allah Ya sanya Al-janna Firdausi ta zamo makomarsa.