Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna ta zaɓi kamfanin jirgin sama na Azman Air a matsayin wanda zai yi jigilar maniyyata Umarah a jihar yayin Umarah mai zuwa.
An cimma wannan matsaya ne bayan ganawar da a ka yi tsakanin tawagar Hukumar Alhazai ta Kaduna da kuma hukumar gudanarwar kamfanin Azman Air, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Hadi Abdulmunaf.
Tawagar hukumar alhazan ta ƙunshi manyan jami’ai da suka haɗa da Daraktan gudanarwa, Alh. Abubakar Alhassan da hadimin Sakataren hukumar Salman Ahmed da shugaban sashen sadarwa, Abubakar Usman da sauransu.
Hukumar Alhazai ta Kaduna na daga cikin hukumomin da NAHCON ta bai wa lasisin gudanar da ayyukan Umarah a ƙasar.
Shugaban tawagar, Alh. Abubakar Alhassan ya ce, “An zaɓi kamfanin Azman Air ne saboda nasarar da ya samu wajen jigilar maniyyatan Jihar Kaduna yayin Hajjin 2022.”