Maniyyata 15,808 ne su ka yi aikin Hajji a shekaru 9 a Yobe — Hukumar alhazai

0
242

Hukumar Alhazai ta Jihar Yobe ta ce, maniyyata 15, 808 ne ta samu nasarar yin jigilarsu zuwa Saudi Arebiya domin aikin Hajji da ga 2013 zuwa 2022.

Shugaban hukumar mai barin gado, Alhaji Bukar Kime ne ya bayyana haka a Damaturu yayin da yake miƙa ragamar shugabanci ga magajinsa, Alhaji Mai-Usman Biriri.

A tuna cewa a ranar 23 ga watan Satumba, 2022, Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya naɗa Biriri a matsayin sabon shugaban hukumar.

jawabinsa na bankwana, Kime ya ce a ƙarƙashin shugabancinsa ne Yobe ta samu lambar yabo daga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) a matsayin jiha mafi zaƙaƙuranci game da Hajjin 2022 da ya gabata.

Kazalika, ya yaba wa ma’aikatan hukumar bisa jajircewarsu a bakin aiki wanda a cewarsa, hakan ya bai wa hukumar ɗaukaka.

Daga nan, sai ya nuna gadiyarsa ga Gwamna Buni dangane da damar da ya ba shi na yi wa hukumar hidima.

A nasa ɓangaren, Biriri ya yi wa Kime fatan alheri a dukkanin fannoni na rayuwa, kana ya yi alƙawarin ɗorawa daga inda ya tsaya.

Sabon shugaban ya nemi haɗin kan ɗaukacin ma’aikatan hukumar don a gudu tare, a tsira tare.