Ɗan Majailsar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar mazaɓar Bakori, Hon. Ibrahim Kurami, ya riga mu gidan gaskiya a birnin Madina, Saudi Arebiya.
Abokin siyasarsa, Alhaji Nasiru Danguga, ya ce Kurami ya rasu ne da misalin ƙarfe biyu na dare agogon Nijeriya bayan fama da taƙaitaccen rashin lafiya.
Bayanai sun ce marigayin ya tafi birnin Madina ne don yin Ummara, tare da cewa a Madina hukumomin ƙasar za su yi masa jana’iza.
Marigayin ya rasu ya bar mata biyu, ‘ya’ya 11 da kuma jikoki uku.
Kurami ya zama ɗan Majlisar Katsina ne bayan nasarar da ya samu a zaɓen cike gurbin da aka yi ran 31 ga Oktoba, 2020, biyo bayan rasuwar wanda ya gada,
Hon. Abdurrazak Ismail Tsiga.