IHR ta damu da rashin maido wa maniyyatan da basu samu yin aikin Hajji kuɗinsu ba

0
255

Kungiyar Masu kawo Rahoton harkokin Hajji da Umrah Mai zaman Kanta, IHR, ta ce abin damuwa ne ganin yadda bayan kwanaki 67 da kammala Hajjin 2022 amma har yanzu Hukumar Hajji ta Ƙasa, (NAHCON) da hukumomin alhazai na jihohi ba su maida wa maniyyatan da suka rasa Hajjin na bana kuɗaɗensu ba.

Cikin sanarwar da ta fitar a jiya Alhamis mai ɗauke da sa hannun shugabanta na ƙasa, Malam Ibrahim Muhammed, IHR ta ce kimanin maniyyatan Nijeriya 3,000 ne suka rasa Hajjin bana saboda wasu ‘yan matsalolin da NAHCON da takwarorinta na jihohi suka fuskanta, duk da maniyyatan sun biya kuɗin tafiya miliyan N2.5.

Sanarwar ta ce duk da takaici da kuma baƙar wahalar da maniyyatan suka fuskanta na rashin samun halartar Hajjin bana, amma har yanzu hukumomin da lamarin ya shafa sun gagara maida wa maniyyatan da kuɗaɗensu.

Sanarwar ta nuna kimanin maniyyata 729 daga Kano, 93 daga Kaduna da kuma 152 Jihar Filato ne suka rasa Hajiin bana sakamakon ƙalubalen da aka fuskanta.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Duk da dai muna sa ran cewa wasu daga cikin maniyyatan za su buƙaci barin kuɗinsu don Hajjn 2023, amma za a iya snin haka ne kawai idan NAHCON da takwarorinta na jihohi suka nuna a shirye suke su maida wa maniyyatan kuɗaɗensu.

“Don haka, abun babu daɗi a ce kwanaki 67 da kammala Hajjin 2022 amma NAHCON da wasu takwarorinta na jihohi sun gaza maida wa maniyyatan da suka rasa Hajjin kudaɗensu,” in ji sanarwar.

Daga nan, IHR ta buƙaci NAHCON da ta cika alƙawarin da ta ɗauka na za ta maida wa maniyyatan da lamarin ya shafa kuɗaɗensu kamar yadda aka ji shugaban hukumar na ƙasa, Barista Zikrullah Kunle Hassan ya alƙaurata a ranar 10 ga Yuli, 2022.

Sa’ilin da yake yi wa manema labarai jawabi a Saudiyya, Shugaban NAHCON ya ba wai maniyyatan da suka rasa Hajjin bana tabbacin hukumar za ta maida musu kuɗaɗensu ba tare da ɓata lokaci ba.

Kazalika, Zikrullah ya sake bai wa maniyyatan da ke ra’ayin barin kuɗinsu don Hajjin baɗi, tabbacin da su a fara idan Allah Ya kai mu lokaci.

IHR ta jaddada aniyarta kan cewa za ta bibiyi lamarin tare da tabbatar da ɗaukacin maniyyatan da suka rasa Hajjin an maida wa kowa kuɗinsa, musamman ga waɗanda ba su da niyar ci gaba da ajiyar kuɗaɗensu a hannun hukumar.

“A ganinmu, ta hanyar maida wa maniyyata kuɗaɗensu da kuma ba su haƙuri kaɗai NAHCON da sauran takwarorinta na jihohi da lamarin ya shafa za iya maido da ƙwarin gwiwar da maniyyata suka rasa a kansu,” in ji IHR.