Da Ɗumi-ɗumi: Hukumar Aljazai ta Katsina ta fara maida wa maniyyatan da suka rasa Hajjin 2022 da kuɗaɗensu

0
266

Hukumar Alhazai ta Jihar Kataina ta ce, ta fara maida wa maniyyatan da ba su samu zuwa Hajjin 2022 ba da kuɗaɗensu.

Cikin wata sanarwar da ta fitar mai ɗauke da sa hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Alh Badaru Karofi, hukumar ta ce, “Ta maida wa rukunin farko na maniyyata kimanin su 101 da suka rasa Hajjin bana kuma suka buƙaci a maida musu kuɗaɗensu, da kuɗaɗensu.”

Daraktan kuɗi na hukumar, Alhaji Sagir Abdullahi Inde shi ne ya wakilci Shugaban hukumar, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki wajen miƙa takardar ceki ga jami’an shiyya na hukumar a madadin maniyyatan da lamarin ya shafa.

Daraktan ya ce kawo yanzu, hukumar ta maida kuɗi miliyan N133,280,000 ga maniyyata 101 da ke rukunin farko.

Ya ƙara da cewa, hukumar za ta ci gaba da maida wa maniyyatan kuɗaɗensu musamma ga waɗanda suke da buƙatar su karɓi kuɗaɗen nasu.