An yaba wa Gwamna Bala kan bai wa harkokin Hajji muhimmanci

0
326

An yaba wa Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad na Jihar Bauchi bisa muhimmancin da yake bai wa harkokin Hajji da maniyyata a jihar.

Wannan yabo ya fito ne daga bakin Sakataren Hukumar Alhazai na jihar, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke birinin Bauchi.

Da yake ƙarin haske game da nasarorin da Gwamnan ya samu a fannin Hajji, Imam Abdurrahman ya ce tun kafuwar gwamnatinsa, Bala ya soma bai wa hukumar kulawar da ta dace.

Ya ce, “Ina yabo da gagarumar gudunmawar da Gwamna Bala Abdulkadir ke bai wa hukumar Hajji tun zuwan gwamnstinsa. Wannan shi ne sirrin nasarorin da muka samu,” in ji shi.

Imam Abdurrahman ya nuna yadda Hukumar Alhazan Jihar Bauchi ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Bala Mohammad ta samu karamci a gida da waje saboda ƙwazonta.

Cikin sanarwar da hukumar ta fitar ranar Alhamis ta hannun jami’in yaɗa labarai, Muhammad Sani Yunusa, Sakataren ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da gina katafaren sansanin alhazai na zamani da lambar yabon da hukumar ta samu daga Independent Hajj reporters (IHR) da sauransu.

Kazalika, ya ce hukumar ta kuma samu lambar karramawa daga wani kamfanin Saudiyya, MAWASIMUL KHAIRAT yayin Hajjin 2022, inda ya jinjina wa Jihar Bauchi kan zama jihar da ke kan gaba daga jihohin Nijeriya wajen kula da sha’anin abincin mahajjata a Makka.

Imam Abdurrahman ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa ɗaukacin masu ruwa da tsaki yayin Hajjin da ya gabata, waɗanda ya ce da gudunmawarsu aka iya cimma dukkan nasarorin da hukumar ta samu.