India za ta rage kuɗin aikin Hajji a 2023

0
433

Indiya ta yanke shawarar rage kudin aikin hajjin 2023 da akalla Rufi dubu100, wato Rs 100,000.

Minista Smriti Irani ne ya sanar da hakan a taron Hajjin Indiya da aka yi a New Delhi a ranar Asabar, 12 ga Nuwamba, 2022.

Taron ya samu halartar mambobin Babban Kwamitin Hajji, tare da shugabannin kwamitocin alhazai na jihohi.

Hakan ya biyo bayan wani gagarumin zargi na cewa an ƙara kudin tafiyar Hajji daga Indiya a bara.

Tafiya zuwa Makkah ta ƙarƙashin Kwamitin Hajji na Indiya ta fi sauki a kan tafiya ta kamfanonin sufuri masu zaman kansu.

Kudaden aikin Hajjin 2022 a hakikanin gaskiya ya fi abin da masu gudanar da yawon bude ido ke karba, kamar yadda mahajjatan suka yi zargin.