Lambar sirri ta masu Umrah ta haifar da babbar matsala a kasar Masar bayan wani lamari da ya shafi dawo wa da alhazai 100 zuwa filin jirgin sama na birnin Alkahira saboda ba su sami “lambar sirri” ta tafiya Umrah ba a shafin neman zuwa Umrah na yanar gizo na Masar ba.
A baya-bayan nan, ma’aikatar kula da yawon buɗe ido ta sanar da cewa wa’adin lambar sirri ta zuwa Umrah na tsawon mako guda ne kawai, inda ta ce Alhazai su fara tafiya zuwa kasa mai tsarki da zarar lambar ta fito.
Hakan ya nuna cewa an dawo da mutane sama da 100 gida kafin su tashi ta jirgin saman Saudiyya sabo da hukumomin da suka cancanta sun nemi su ba su lambar sirri amma ba su da ita.
Masar ta kaddamar da lambar sirri ta Umrah ta hanyar yanar-gizo tun daga daga wannan shekara, a cewar Noura Ali, shugaban kwamitin yawon bude ido na majalisar, wanda ya bayyana cewa yawancin mahajjata sun yi amfani da ita.
A cewar Mustafa Faragha, kwararre kan harkokin yawon bude ido, mahajjacin da ya karbi lambar shaidar zuwa Umrah, hakan zai tabbatar da ingancin bizar sa ta Umrah, da ingancin shirin da kuma kammala kulla dukkan ayyukan da suka shafi tafiya Umrah.,
A cewar Mustafa Faragha, lambar sirrin na baiwa hukumomin da suka dace kamar ma’aikatar yawon bude ido a filayen tashi da saukar jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa damar duba bayanan matafiya.
Bibiyar mahajjaci a lokacin aikin umrah da gaggawar shiga tsakani don warware duk wata matsala, da kuma duba mahajjaci idan aka samu matsala da gajiya, har ya dawo kasarsa lafiya na yiwuwa ne ta hanyar lambar sirri..