Wata alhajiyar Ummara ta haihu a Masallacin Ma’aiki a Madina

0
186

Wata mata da a ke kyautata zaton ta je yin Ummara ne, ta haihu a Masallacin Harami na Annabi Mai Tsira da Aminci.

Jami’an ƙungiyar agaji ta Red Crescent ne su ka karɓi haihuwar ta ta bayan naƙuda ta kama ta a Masallacin Mai Tsarki.

Shafin da ke kula da masallatai biyu masu daraja na Saudiyya, mai suna Haramain Sharifain ne ya wallafa labarin a Facebook a jiya Juma’a.

Jami’an Red Crescent din sun je ne bayan kiran gaggawa da aka yi musu.

Bayan nan ne kuma sai aka kai mai jegon da jaririnta wani asibiti Jibril Health Center don ci gaba da kula da su.

Sai dai shafin bai bayyana ko da ga wacce nahiya ko ƙasa mai jegon ta fito ba, sai dai kuma ha ce mace matar ta haifa.

Mahaifin jaririyar tuni ya raɗa mata suna Taiba, kamar yadda shafin ya ruwaito.