Ganduje ya bukaci a hukunta NAHCON bisa gazawarta wajen aikin Hajjin 2022

0
232

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bincika tare da hukunta shugabannin Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON bisa abin da ya kira da gazawarsu wajen ingantaccen shirin zuwa aikin Hajji na bana.

Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yabke karbar rahoton aikin hajjin bana daga Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano.

Gwamna Ganduje yace tun da ya zama gwamnan kano bai taba ganin yadda hukumar ta yi rashin tsari ba kamar shekarar data wuce, Inda yace akwai rashin gaskiya da kwarewa a aiyukan shugabannin hukumar NAHCON a wannan karo.

” Sun cuci alhazai sun cuci ma’aikata, sun kawo chanje-chanje marasa ma’ana, sun kawo rashin gaskiya da son rai sun kasa kai alhazai kuma sun cucesu”. Inji Ganduje

” Sun bamu jirgin da zai yi jigilar alhazan mu, mun fada musu ba ma so. Ni da kai na ma sai da naje har ofishin hukumar da ke abuja na Kuma koka musu suka ce min zasu gyara, Amma bayan tahowa ta suka ki chanzawa”.

Ganduje ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da majalisar wakilai ta kasa da su bincika domin daukar matakan da suka dace don hana faruwar hakan a nan gaba.

Ya kuma yabawa hukumar Jin dadin alhazai ta jihar Kano bisa yadda su ka gudanar da kyakyawan tsari a aikin hajjin daya gabata.