IHR za ta shirya Babban Taro kan Shirin Adashin Gata na Hajji

0
211

Cibiyar Independent Hajj Reporters (IHR) ta ba da sanarwar za ta shirya taron ƙasa da ƙasa nan ba da daɗewa ba domin tattauna abin da ya shafi tsarin Shirin Adashin Gata na Hajji, wato HSS a taƙaice.

Cibiyar ta ce, la’akari da ce-ce-ku-cen da shirin na HSS ya haifar a tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin Hajji a Najeriya, hakan ya sa za ta shirya wannan taron domin wayar da kan al’umma game da tsarin.

IHR ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun shugabanta na ƙasa, Ibrahim Muhammed.

Sanarwar ta nuna za a shirya wannan gagarumin taron ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), da Majalisar Hukumomin Alhazai na Jihohi da da sauran abokan hulɗa.

A cewar sanarwar, taron mai taken: Taron ba da shawarwari game da Shirin Adashin Gata na Hajji, za a gudanar da shi ne a Abuja nan ba da daɗewa ba.

Sanarwar ta ce, “Tun bayan da aka ƙaddamar da shirin a hukumance a ranar 5 ga Oktoba, 2020, ya haifar da ra’ayoyi mabambantan a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki, lamarin da wasu hukumomin alhazai na jihohi suka ce ba su gamsu da tsarin aiwatar da shirin ba.”

IHR ta ce, ta yarda cewa babu wata hanya da za a yi amfani da ita a madadin wannan wajen tanadin guzirin tafiya Hajji na dogon lokaci, musamman idan aka yi la’akari da irin ƙalubalen da ake fuskanta daga tsarin kalandar shekara guda da ake gudanarwa a aikin Hajjin Najeriya.

Don haka ta ce akwai buƙatar a yi nazari mai zurfi kan tsarin muddin ana son ganin tsari mai armashi wanda zai taimaka wajen inganta sha’anin hidimar alhazan Najeriya da kuma samar da daidaiton kuɗi ga harkar Hajji da Umarah a Najeriya.

Ta ƙara da cewa, Shugaban hukumar NAHCON ya faɗa yayin taron masu ruwa da tsaki na aikin Hajji na 2022 cewa, za a gudanar da aikin Hajjin na bana ne ta hanyar amfani da tsarin Adashin Gata da kuma tsarin biya yanzu, tafiya yanzu wajen yi wa maniyyata rajista.

Ta ce, taron zai ba da dama ga manyan masu ruwa da tsaki kamar hukumomin alhazai na jihohi da masu gudanar da aikin Hajji da Umarah da kuma cibiyoyin kuɗin da abin ya shafa su haɗu su tattauna domin cimma matsaya kan tsari ingantacce na gudanar da Shirin Adashin Gata na Hajji a ƙasar.

Sanarwar ta nuna cewa, tun da HSS abu ne da ya shafi maniyyata, don haka za a bai wa maniyyatan da ke cikin tsarin da ma masu shirin shiga, damar shiga taron ta bidiyo don a yi da su.

“Taron zai tattaro manyan masana hada-hadar kuɗi na aikin Hajji daga sauran ƙasashe kamar Malaysia, Indonesiya da kuma fitattun masanan Najeriya da suka halarci kafa Dokar NAHCON, don yin ƙarin haske game da Sashe na 7 na Dokar NAHCON, sashen da ya bai wa hukumar ikon kafawa da kuma kula da Shirin Adashin Gata na Hajji.

IHR ta yi ra’ayin cewa rashin aiwatar da shirin HSS cikin nagartaccen tsari na daga manyan dalilan da suka haifar da ƙalubalan da aka fuskanta yayin Hajjin bana.

Kazalika, ta ce taron yini ɗayan, zai kuma tattauna hanyoyi da matakan da za su taimaka wajen ingantawa da bunƙasa ayyukan gudanar da Hajji a Najeriya.

Haka nan, taron zai yi la’akari da kurakuran da aka samu yayin Hajjin 2022 don ɗaukar matakin hana aukuwar hakan a gaba.

IHR ta ce, a matsayinta na cibiyar farar hula wadda babban manufarta ita ce tabbatar da yanayi mai armashi ga maniyyata, za ta ci gaba da bibiyar lamurra don tabbatar da maniyyata na samun kulawar da ta dace yayin Hajji da Umarah a gida da waje.