Shirye-shiryen Hajjin 2023: Ma’aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya da Hukumar Hajji ta Nijeriya (NAHCON) za su yi tattaunawa ta musamman ta kafar ‘Zoom’

0
410

A matsayin wani mataki na shirye-shiryen Hajjin 2023, Ma’aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya ta sanar da Hukumar Hajji ta Nijeriya (NAHCON) cewa, za su yi tattaunawa ta musamman ta kafar ‘Zoom’ ya zuwa ranar 21 ga Disamban 2022.

Sanarwar na ƙunshe ne cikin wasiƙar da Saudiyya ta aike wa NAHCON ɗin ta hannun Ma’aikatar Harkokin Waje.

Sanarwar ta ce, tattaunawar wani tsani ne na ƙoƙarin cimma rattaba hannu a Yarjejeniyar Fahimtar Juna tsakanin ƙasashen biyu dangane da abin da ya shafi Hajjin 2023.

A cewar sanarwar, tattaunawar za ta gudana ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe agogon Saudiyya, daidai da ƙarfe 8:30 agogon Nijeriya.

A hannu guda, mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda, ta bayyana cikin sanarwar da ta fitar ranar Asabar cewa, farashin kujerar Hajjin baɗi na daga cikin batutuwan da za a tattauna yayin ganawar.