Tawagar maza da mata 60 daga Kungiyar Nakasassu ta Al Thiqah Club da ke birnin Sharjah, Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE sun tafi kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah, karkashin kulawar kungiyar agaji ta Sharjah Charity International da kuma gidan agaji na Sharjah.
Wannan shiri wani bangare ne na hadin gwiwar kungiyar Al Thiqah Club don nakasassu da cibiyoyin jin kai a Sharjah a cikin shirye-shiryen kungiyar, da nufin habbaka imanin mambobin ta.
Dr. Tariq Sultan bin Khadim, shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar ta Al Thiqa Club ya bayyana cewa, a na kokarin bunkasa dukkanin harkokin wasanni, al’adu da zamantakewar ‘ya’yan kungiyar, kuma ra’ayin wannan Umrah ya zo ne don bunkasa Imani na addini na mambobi ta hanyar ziyartar wurare masu tsarki, ɗebe musu kewa, da shigar da su cikin al’umma.
Ya yi godiya tare da jinjina wa duk wanda ya ba da gudummawar wannan shiri, wanda ke da tasiri sosai ga nakasassu.