Hukumar Alhazai ta Jihar Nasarawa, ta roki Gwamnatin jihar da a ƙara mata kasafin kudi na 2023 da ta gabatar don ba ta damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Hukumar ta buƙaci hakan ne bisa la’akari da yiwuwar ƙaruwar adadin maniyyatan jihar yayin Hajjin 2023.
Sakataren hukumar, Malam Idris Ahmad Almakura ne ya yi wannan roƙo sa’ilin da ya bayyana a gaban Kwamitin Alhazai na Majalisar Jihar da ke Lafia, babban birnin jihar, don kare kasafin hukumar na baɗi.
Almakura, wanda ya jagoranci tawagar hukumar ya ce, kasafin hukumar na 2023 bai kai na 2022 ba duk da ana hasashen fuskantar ƙalubale a ayyukan Hajjin 2023.
A cewarsa, tawogar Jihar Nasarawa, yayin Hajjin 2022 ta ƙunshi kimanin alhazai 800 ne, sannan ya zuwa Disamban bana hukumar ta yi wa maniyyata kimanin 1,600 rijista dangane da Hajjin 2023.
Almakura ya jaddada cewar hukumar na sa ran samun maniyyata a 2023 fiye da na 2022, don haka ya ce akwai buƙatar ƙara kasafin hukumar na 2023 domin ba ta damar sauke nauyin da ke kanta yadda ya kamata.
A nasu jawabin, mambobin kwamitin Majalisar, Hon. Muhammad Agah Muluku da takwaransa Hon. Salihu Iyimoga, sun yi na’am da buƙatar hukumar.
Shugaban Kwamitin, Hon. Aliyu Ibrahim Nana, ya ce za su yi nazarin buƙatun da hukumar ta gabatar musu da zummar magance su don samun nasara a Hajjin 2023.
Kwamitin ya nuna gamsuwarsa dangane da irin rawar da hukumar ta taka yayin a Hajjin 2022.