Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina, ta fara yi wa maniyyatan Hajjin 2023 a jihar rijista.
Shirin wanda aka fara aiwatar da shi a ranar Juma’a, ya biyo bayan damar da Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari ya bai wa hukumar ne kan ta soma shirye-shiryen Hajjin baɗi kamar dai yadda Shugaban Hukumar, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ya bayyana.
Hukumar ta ce Gwamna Masari ya amince ta fara yi wa maniyyata rijista da karɓar kuɗaɗensu a faɗin jihar.
Suleiman ya ce maniyyata a jihar na iya soma biyan kaso mafi ƙaranci na Naira miliyan ɗaya da rabi (N1.5m) yayin yin rijistar, sannan a ƙarasa biyan cikon Naira miliya N1 ya zuwa ƙarshen watan Janairu mai zuwa, wanda jimillar kuɗin ya kama miliyan N2.5 ke nan.
Ya ƙara da cewa, maniyyata za su biya kuɗin ne a cikin asusun banki na hukumar.
Ya ce shirin yin rijistar zai gudana ne a ofishin hukumar da ake da su a shiyyoyi bakwai a faɗin jihar, da suka haɗa da Katsina, Funtua, Malumfashi, Dutsinma, Kankia, Daura da kuma Mani.
Haka nan, ya ce za a bi tsarin wanda ya fara zuwa, shi za a fara yi wa rijista.
A cewar jami’in, Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta bai hukumomin alhazai na jihohin umarnin su fara yi wa maniyyatan Hajjin 2023 rijista kafin lokacin da za a fitar da tsare-tsare da kuma kason kujerun da kowace jiha za ta samu.
A ƙarshe, Suleiman ya yi kira ga maniyyatan jihar da su tuntuɓi jami’an da aka naɗa don yin rijistar a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso gudun kada a samu akasi