An fara karɓar kuɗin aikin Hajjin 2023 a Kano

0
2163

A yau Litinin ne hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Kano ta Fara karbar kudin Adashin Gata daga hannun Maniyyata aikin Hajjin Shekara ta 2023.

An fara karɓar kuɗi mafi ƙaranci kimanin Naira miliyan 1.5.

An fara biyan kuɗin ne ta takardar ajiye kuɗi ta banki.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ya fitar, duk maniyyacin da ya biya kuɗin, zai bada hotunan sa guda 6.

Sanarwar ta ƙara da cewa nan gaba kaɗan kuma hukumar za ta buɗe karɓar kuɗin aikin hajji ta tsarin adadin gata, wanda a ka fi sani da Hajj Savings Scheme.