Hajjin 2023: Rukunin farko na maniyyata zai sauka a Saudiyya ran 21 ga Mayu — Saudi

0
446
????????????????????????????????????

Ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta tsara jadawalin jigilar alhazai ta shekarar 2023 zuwa kasar Saudiyya a ranar 1 ga watan Dhul Qa’adah wanda ya yi daidai da 21 ga watan Mayun 2023.

Ma’aikatar aikin hajjin ta bayyana hakan ne yayin wani taron share fage da hukumar Hajji da Umrah ta Afirka ta Kudu (SAHUC).

Ma’aikatar ta kuma tabbatar da cewa, ba za a kayyade yawan shekaru ga maniyyatan da ke son zuwa aikin Hajjin shekarar 2023 ba.

Sanarwar ta ce an gayyaci SHUC zuwa kasar Saudiyya nan da mako na 2 ga watan Janairu domin ci gaba da ganawa da ma’aikatar aikin Hajji ta Saudiyya.

Manyan batutuwan manufofin hajjin 2023 kamar yadda SHUC ta buga su ne kamar haka.

Babu iyaka ga Mahajjata na 2023

Za a buƙaci rigakafin zazzabin shawara, sanƙarau da takaddun rigakafin covid.

Ba za a buƙaci gwajin cutar korona ba da dai sauransu.