Kasar Saudiyya ta maido wa Najeriya kudi Riyal 542,033, kwatankwacin Naira miliyan 107,864,567 a matsayin kudin abincin da ba ta samu ciyar da alhazan ƙasar ba yayin Hajjin 2022.
Najeriya ta karbi kudin ne ta hannun Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON).
Cikin sanarwar da ta fitar ta bakin Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Hukumar, Mousa Ubandawaki, NAHCON ta ce kamfanin kula da alhazann Afirka na Mutawwif ne ya bayar da kudin sakamakon rashin ciyar da alhazan kasar yadda ya kamata yayin Hajjin bana.
Sanarwar ta ce, hakan ya biyo bayan korafe-korafe da NAHCON ta rubuta wa kamfanin ne na tunatar da shi rashin ingancin tsarin ciyar da alhazan da aka fuskanta a lokacin aikin Hajjin.
Idan dai za a iya tunawa, rahotanni sun nuna yadda alhazan Nijeriya su ka fuskanci matsalar abinci na wasu kwanaki yayin Hajjin na 2022.
Lamarin da ya sa NAHCON ta rubuta wasikar korafi zuwa ga kamfanin da lamarin ya shafa don daukar matakin da ya ce.
Da ya ke ƙarin haske game da lamarin, Shugaban NAHCON na Kasa, Alh. Zikhrullah Kunle Hassan, ya ce maido da kudin abin ayaba ne.
Ya ce hakan na nuni da yadda hukumar ta zage dantse wajen ganin an gyara kura-kuran da aka aikata wa alhazan Najeriya a yayin Hajjin 2022.
Daga nan, ya nuna godiyarsa ga Kamfanin Mutawwifs na maido da kudin da ba su yi aikinsa ba.
Mutawwifs kamfanin Saudiyya ne mai kula da sha’anin masauki da abinci da kuma zirga-zirgar alhazan kasashen Afirka a Muna da Arafat a lokacin Hajji.