Hajjin baɗi: Maniyyata za su fara ajiye Naira miliyan 1.5 a Jihar Cross River

0
454

Hukumar Jin daɗin Alhazai Musulmai ta Jihar Cross River ta sanar da za ta fara karɓar kashin farko na kuɗin Hajjin 2023.

Hukumar ta sanar da cewa za ta fara karɓar kuɗin ne, da ya kai Naira miliyan 1.5, ta hanyar da ta saba karɓa da ga maniyyata da kuma adashin gata na Hajji.

A sanarwar da Sakataren Hukumar, Alhaji Abdullahi Orok ya fitar, hukumar ta ce maniyytan za su ajiye kuɗin ne ta banki.

Sanarwar ta ce Shugaban Hukumar, Rabilu Abdullahi Maimaje ne ya sanar da hakan a yayin hira da manema labarai a wajen bikin gargajiya na Calabar.

Ya ce a ranar Juma’a, 30 ga watan Disamba za a fara karɓar kuɗaɗen, inda ya ƙara da cewa maiyyaci zai biya a ƙalla Naira miliyan 1.5.