Kamfanin jiragen sama na Saudiyya zai fara jigila daga Kano zuwa Jeddah ta mako-mako”

0
290

Kamfanin Jiragen Sama na Saudiyya ya sanar da shirinsa na komawa jigaila a filin jirgin saman Aminu Kano da ke Kano daga ranarq Talata, 3 ga Janairu, 2023.

Wata wasika mai dauke da kwanan watan 29 ga watan Disamba ta aikewa ALL TRAVEL AGENCY AND NANTA, inda ta ce za a fara gudanar da jigilar ne da ranaku uku na mako ( Talata, Alhamis da Asabar) tare da tashi daga Jeddah da karfe 12:50 na rana sannan kuma ya sauka a Kano da karfe 15:40 na yamma.

Zai kuma sake tashi daga karfe 18:15 suka tashi Kano suka isa Jidda da karfe 00:40.

Wasikar ta kuma bayyana cewa masu dauke da bizar Umrah su kai rahoto da fasfo na zahiri, tikiti da biza don tantancewa da amince wa.