Hukumar gudanarwar Haramin Makka ta samar da ɗakin rarraba Alkur’ani

0
383

Babban ofishin kula da harkokin masallatan Harami biyu na kasar Saudiyya, wanda sashen kula da harkokin kur’ani mai tsarki ya wakilta, ya kebe wani ɗaki a harabar masallacin da ke gabashin masallacin Harami don rarrabawa da kuma bayar da kyautar kwafin kur’ani mai tsarki, wanda hakan ya kara habaka adadin wuraren da aka amince da su zuwa uku.

Shugaban sashen Hamzah Al-Salimi ya bayyana cewa a kullum ana raba kwafin kur’ani mai tsarki har guda 2,500 a matsayin kyauta a cikin babban masallacin ‘kasar.

Sashen ya na ba da kwalaye 750 don rabawa a kullum tare da kwafin kur’ani mai tsarki 75,000 a kowane wata, baya ga baiwa makafi kwafin kur’ani mai tsarki guda 30 mai ɗauke da na’urar da makafi za su iya karanta wa – SPA