Mata sun fara tuƙin jirgin ƙasa a Saudiyya

0
480

Biyo bayan wasu sauye-sauye da aka samu a kasar Saudiyya, mata sun fara tuƙa jirgin ƙasa na Makkah zuwa Madina a karon farko a tarihin masarautar.

Wani rahoto da jaridar Saudi Gazette ta fitar ya nuna cewa rukunin farko na mata 32 direbobin jirgin kasa na Haramain Express sun samu cikakken horon sarrafa daya daga cikin jiragen kasa mafi sauri a duniya.

Hukumar jirgin ƙasa ta Saudiyya ta yi wani sha’ani na tarihi a baya-bayan nan, inda ta nuna fina-finai da ke nuna mata na ɗaukar horo tare da bada bayanan abubuwan da su ka koya.

Matan sun kuma yi murna da samun nasarar zama mata na farko da ke tuka jirgin kasa a yankin Gabas ta Tsakiya, inda suka ce jigilar alhazai da masu ziyara yana ba su kwarin guiwar yin aiki cikin kulawa sosai.

Tun da fari, an saki sanarwar ɗaukar direbobin jirgin dozin uku, wanda ya jawo hankalin masu neman aiki 28,000 yayin da damar yin aiki ga mata ya ninka a cikin shekaru biyar da suka gabata a ƙarƙashin shirin hangen nesa na Masarautar 2030 wanda ke da nufin rage dogaro da mai.

A cikin 2017, Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya ba da sanarwar sauye-sauye masu tsauri yayin da aka baiwa mata damar tuka motoci a karon farko.

Masarautar ta kuma baza jami’an tsaro mata a wurare masu tsarki domin kula da masu ibada da mahajjata tare da tabbatar da an bi dukkan matakan kariya a cikin masallacin Harami.