Saudiyya ta raba naman hadayar Hajji ga mutane miliyan 30 a kasashe 27

0
194

Aikin Saudiyya na Amfani da Dabbobin Layya, wanda kuma aka fi sani da Adahi, ko Hadaya, kwanan nan ya raba naman hadaya ɗin mai yawa ga kasashe da dama.

Rabon da aka yi ya haɗa da dabbobin hadaya guda 3,000 da aka aika kowacce zuwa kasashen Azerbaijan, Mali, Mozambique, Chadi da Gambia, 4,000 zuwa Nijar da 5,000 zuwa Djibouti.

Wannan shiri dai na zuwa ne a matsayin tsawaita ayyukan agajin da jin-ƙai da masarautar kasar ke aiwatarwa a kasashe da dama karkashin umarnin Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman.

Tsarin rarrabawar ya ƙunshi ƙungiyoyi da daban-daban na jin-ƙai, ƙarƙashin kulawa da bin diddigin kwamitin da gwamnatocin da su ka amfana su ka kafa.

Wakilan aikin daga kungiyar Bankin Raya Musulunci da jami’ai a gwamnatocin kasashen su ma sun halarci aikin rabon.