A jiya Alhamis ne mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya ƙaddamar da fara amsar kuɗin Hajjin 2023.
Yayin ƙaddamar war, Dr. Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ya bayyana cewa maniyyata za su biya kuɗaɗen ne ta hanyar amsar takardar banki daga jami’an hukumar alhazai na kananan hukumomi.
Ya yi bayanin cewa biyan karɓar takardar, maniyyatan za su sanya kudin a banki, wanda a yanzu ana amsar mafi karanci N1,500,000.
“Maniyyata na iya biyan har zuwa N2,500,000, kafin ayyana hakikanin kudaden hajjin bana,” in ji sanarwa mai ɗauke da sa hannun Ibrahim Shehu Giwa, Special Assistant to the Executive Secretary.
Dr. Arrigasiyyu, a cewar sanarwar, ya kara da cewa, kada wani maniyyaci ya baiwa wani kudi a hannu, kowaye, ta banki za’a tabbatar an biya, sannan an inganta tsari a bana, ta yadda za’a kaucewa karkatar da kujeru ga wasu ɗaiɗaikun mutane.
A bana, Nijeriya ta samu gurbin mutane 95,000 ne wanda za su tafi aikin hajji insha Allah, kuma an cire takunkumin da aka sanya a bara.