* Makon gobe za ta soma maida wa maniyyatan 2022 kuɗaɗensu
A matsayin ɓagaren na shirye-shiryen Hajjin 2023, Hukumar Alhazai ta Jihar River ta fara yi wa maniyyata rijista.
Jagoran hukumar, Alhaji Diepriye Abdulrazak, ya sanar cewa hukumar ta tsayar da miliyan N2.5 a matsayin mafi ƙarancin kason da za a iya soma biya ga masu niyyra zuwa hajjin bana a jihar.
Da yake yi wa Hajj Reporters ƙarin haske, Abdulrazak ya ce an soma yi wa maniyyata na bana rijista kuma ya zuwa mako mai zuwa hukumar za ta fara maida wa maniyyatan da ba su samu zuwa Hajjin 2022 ba kuɗaɗensu.