Hajjin 2023: Miliyan N2.6 ne mafi ƙarancin abin da maniyyaci zai iya fara biya a Oyo – Hukuma

0
213

* Ta miƙa rahoton Hajjin 2022 ga Gwamnan jihar

Hukumar Alhazai ta Jihar Oyo, ta ce Naira miliyan 2.6 shi ne mafi ƙarancin kuɗin da maniyyata Hajjin bana a jihar za su iya fara biya a matsayin ajiya kafin cikawasa daga bisani.

Shugaban hukumar (na ɓangaren kula da maniyyata Musulmi), Farfesa Sayed Malik ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci tawagar hukumar zuwa miƙa rahoton harkokin Hajjin 2022 a jihar ga Gwamnan jihar, Injiniya Seyi Makinde.

Sa’ilin da yake karɓar rahoton a Fadar Gwamnati da ke Agodi, Ibadan babban birnin jihar, Gwamnan ya yaba wa Shugaban da tagawarsa da ma sauran ma’aikatan hukumar bisa nasarar da suka samu yayin Hajjin bara.

Ya yi kira gare su da su ƙara himma a bakin aiki, kana su guji rashawa wadda ka iya ɓata mutuncin jihar a idon duniya.

Daga nan, ya buƙaci hukumar da ta fara shirye-shiryen Hajjin 2023 a kan kari don guje wa samun kowane irin akasi.

Tun farko da yake jawabi, Shugaban hukumar, Farfesa Malik ya sha alwashin aiwatar da duka umarnin da gwamnan ya bayar dangane da maniyyatan jihar su 150 da ba su samu zuwa Hajjin 2022 ba.

“Duk wani maniyyacin Jihar Oyo da ya rasa Hajjin 2022 kuma yake buƙatar a maida masa da kuɗinsa, za a yi hakan ba tare da rage ko sisi ba,” in ji Malik.

Ya ƙara da cewa, waɗanda kuma ke da niyyar barin kuɗin don Hajjin 2023 da su za a fara, sannan ba za a buƙaci su biya ƙarin ko kwabo ba kan abin da suka riga suka biya.

Ya ce, al’adar hukumar ce mayar wa maniyyatan jihar da rarar kuɗin da aka samu tun kafuwar gwamnatin jihar mai ci.

A cewarsa, “Bayan cire duka abin da ake buƙata a biya na aikin kula da mahajjatan da suka sauke farali bara, hukumar ta mayar wa mahajjatan miliyan N37,909,556.66 a matsayin rarar da aka samu yayin Hajjin 2022 inda kowannensu ya samu N62,556.01.”

A hannu guda, Shugaban hukumar ya ce hukumar ta tsayar da N2.6 a matsayin mafi ƙarancin abin da maniyyatan jihar za su iya fara biya don Hajjin 2023.

“Maniyyata Hajjin 2023 a jihar za su iya fara biyan kuɗinsu a cikin asusun bankin hukumar da aka tanadar musamman don hakan,” in ji shi.