Hajjin 2023: Najeriya ta samu kujera 95,000, in ji NAHCON

0
441

A ci gaba da shirye-shiryenta na Hajjin 2023, Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta yi rabon kason kujerar Hajji ga jihohi da kamfanoni sufurin masu yawo shaƙatawa.

NAHCON ta ce kujeru 95,000 ta samu daga Ma’aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya don Hajjin 2023.

Hukumar ta bayyana hakan ne ranar Litinin bayan da suka kammala rattaɓa hannu a yarjejeniyar fahimtar juna a Makkah.

Sanarwar da NAHCON ta fitar mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Mousa Ubandawaki, ta ce “Ma’aikatar za ta raba kujera 75,000 ga hukumomin alhazai na jihohi, sannan ragowar 20,000 a tsakanin kamfanonin yawon shaƙatawa masu lasisi.

“Ɗaya daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa shi ne tabbacin samun kujerun Hajji 95,000 ga Najeriya inda jihohi 36 na ƙasar haɗa da cibiyoyi da hukumomi ciki har da Birnin Tarayya da sojoji suka samu 75,000.

“Sannan kamfanin yawon shaƙatawa suka tashi da kujeru 20000,” in ji sanarwar.