Yanzu-yanzu: Nijeriya da Saudiyya sun sa hannu kan yarjejeniyar aikin hajjin 2023

0
159

Tawagar Nijeriya da ta isa Saudiyya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU), tare da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Masarautar dangane da aikin Hajjin 2023.

Yarjejeniyar ta kasance ta ka’idojin da za a yi amfani da su don aikin Hajjin 2023.

A wata sanarwa da shugaban yada labarai na hukumar alhazai ta kasa NAHCON, Mousa Ubandawaki ya fitar a jiya Lahadi, ta ce tawagar Najeriyar ta na karkashin jagorancin karamin ministan harkokin wajen kasar, Zubair Dada l.

Ubandawaki ya ce tawagar ta kuma hada da, Sanata Adamu Bulkachuwa, shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin kasashen waje, Abubakar Nalaraba, shugaban kwamitin majalissar kan aikin hajji, shugaba/shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan, da kuma wasu daga cikin mambobin hukumar da ma’aikatan NAHCON.