Saudiya ta cire duk wasu sharuɗɗa da kariya, inda za a yi Hajjin 2023 kamar yadda aka saba

0
392

Ƙasar Saudiyya za ta yi maraba da maniyyatan da za su fara aikin Hajjin bana da adadinsu ya kai na yadda aka saba kafin bullar annobar COVID-19, a cewar Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dr. Tawfiq Al-Rabiah.

Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Masarautar za ta soke ƙayyade shekarun da ake bukata ga mahajjata, bayan shekaru uku na takunkumi don dakile cutar ta COVID-19.

Al-Rabiah ya bayyana haka ne a jiya Litinin a wurin bude taron “Expo Hajj”, taron baje kolin ayyukan hajji da umrah da ake gudanarwa a Jeddah daga ranar 9-12 ga watan Janairun 2023.

Ya ce: “Daga lokacin aikin Hajjin bana za mu ba da damar hukumomin gudanar da hidimomin aikin Hajji daga sassan duniya da su amince da duk wani kamfani da ke da izini don samar da ayyuka ga mahajjata a Masarautar.

“Tare da abokan aikinmu, mun ƙaddamar da dandalin NUSK don sauƙaƙe hanyoyi da haɓaka ayyuka da hidimomi don jin daɗin mahajjata,” in ji shi.