DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamna Abdulrazaq ya naɗa sabon shugaban hukumar alhazai na Kwara

0
372

Gwamnan jihar Kwara, Alh Abdulrazaq Abdulrahaman ya amince da nadin Alh Abdulsalam Abdulkadir a matsayin sabon babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kwara a Ilorin.

Wata ‘yar gajeriyar sanarwa da aka aike wa HAJJ REPORTERS ta ce “nadin na nan-take ne.”

Kafin nadin nasa l, Alh Abdulsalam Abdulkadir ya kasance kwararren akanta mai ofishi a jihar Legas.

Nadin dai ya sauke tsohon babban sakataren hukumar, Barr Abdulganiyu Ishola Ahmed daga mukaminsa.

An haifi Abdulsalam Abdulkadir a ranar 1 ga Yuli, 1964 a Unguwar Ilorin Pakata ta Jihar Kwara.