Duba da sabbin canje-canje a gudanarwan aikin hajji, da kuma sabanin fahimta da akan samu yayin gabatar da aikin hajji, Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Dr Yusuf Yakubu Arrigasiyyu ta shirya taron jin ra’ayin Masu ruwa da tsaki, Musamman Malamai don gabatar musu da littafin “Jagoran Mahajjata” da aka hada fahimta waje daya, don samun matsaya daya na hukumar kan hukunce-hukuncen aikin Hajji, bayan inganta littafin da kwamitin masana yayi.
Taron wanda ya sami halartan wakilcin Malamai da masu bita daga dukkan kananan hukumomi 23, da wakilan jami’an hukumar kiyaye fasa kwauri (Custom), jami’an hukumar shige da fice (Immigration), ma’aikatan lafiya da sauran masu ruwa da tsaki.
Wannan na nufin cewa, daga yanzu duk fahimta ko fatawa gameda aikin Hajji za’a aje shi gefe guda, ai aiki da matsayar hukumar alhazan na jihar Kaduna, wanda Malamai suka dauki fahimta mafi kusa da da sauki da daidai.
Ibrahim Shehu Giwa,
Special Assistant to the Executive Secretary,
January 11th, 2022.