Hajjin 2023: Alhazan Afirka za su yi amfani da tanti mai hawa-biyu a Mina

0
208

A karon farko, wasu alhazan Afirka da ba ƴan ƙasashen Larabawa na nahiyar ba za a ba su masauki a cikin tanti mai hawa biyu a yayin zaman Mina a Hajjin 2023 mai zuwa.

Shugaban kungiyar Masu yi wa Alhazan Afirka da ba Larabawa ba, Ahmad Sindi ne ya bayyana hakan a yayin bikin baje- kolin Hajjin 2023 da aka kammala a Jeddah, Saudi Arebiya.

Yayin da ya ke ba da tabbacin gudanar da aikin hajji ingantacce, musamman a fannin gudanar da ayyuka masu inganci ga mahajjata daga kasashen Afirka da ba na Larabawa ba, Sindi ya ce a shirye su ke su kyautata aikin Hajjin 2023 fiye da na shekarun baya.

Ya kuma bayyana cewa, hukumarsa a wani yunkuri na samar da karin dakuna da sarari ga mahajjata, ta amince da yin amfani da gadaje masu hawa-biyu a Mashair ga wasu kasashe a bana.

Hukumomin Saudiyya sun kaddamar da wani tanti mai hawa biyu a Mina a shekarar 2019, amma ba a fadada ayyukan ga dukkan kasashen da ke halartar aikin Hajji ba.