Kwamishina a NAHCON ya rasu

0
168

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta sanar da rasuwar kwamishinanta na yankin arewa maso yamma, Alhaji Umar Garba.

Sanarwar, wacce ta fito da ga hannun mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai a hukumar alhazai ta jihar Neja a yau Lahadi, d ta tabbatar da cewa Alhaji Umar Garba ya rasu ne da sanyin safiyar yau, 15 ga watan Janairun 2023 bayan gajeruwar rashin lafiya.

Independent Hajj Reporters ta bi sahun NAHCON wajen jimamin rasuwar Alhaji Umar Garba, tare da mika ta’aziyya ga iyalai da abokan marigayin.

Allah ya jikan sa da rahama amin