Hajjin 2022: IHR ta yaba wa Gwamnan Oyo kan maida wa maniyyata kuɗaɗensu

0
261

Kafar Independent Hajj Reporters (IHR) mai bibiyar harkokin Hajji da Umarh a Nijeriya da ƙetare, ta yaba wa Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, dangane da irin kulawar da ya bai wa maniyyatan da suka rasa Hajjin 2022 a jiharsa.

Yabon ya biyo bayan umarnin da Gwamnan ya bai wa Hukumar Alhazan Jihar kan kada ta cire ko kwabo daga kuɗin maniyyatan jihar da suka rasa Hajjin bara kuma suka nemi a maida masu kuɗaɗensu.

Sanarwar da IHR ta fitar ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun babban jami’nta na ƙasa, Malm Ibrahim Muhammed, ta nuna kafar na sane da cewa an cire wani kaso daga kuɗaɗen da maniyyatan da suka rasa Hajjin 2022 suka biya a wasu jihohi.

Kafar ta ce jin irin kalaman da Makinde ya yi a lokacin da yake karɓar rohoton Hajjin 2022 a Fadar Gwamnatin jihar da ke Ibadan abin a yaba ne.

Haka nan, gwamnan ya ce waɗanda ke ra’ayin barin kuɗinsu don Hajjin bana daga maniyyatan da lamarin ya shafa da su za a fara.

Ya kuma ce babu ƙarin kuɗin da za su biya a kan abin da suka biya bara ko da kuwa ya faru cewa kuɗin kujerar bana ya ɗara na bara.

“Wannan na nuni da cewa Gwamnatin Jihar Oyo za ta nuna bambanci mai ma’ana dangne da Hajjin 2023 ga maniyyatan jihar da suka rasa Hajjin 2022. Wannan abin a yaba ne,” in ji IHR.

Daga nan, IHR ta yi kira ga masu faɗa a ji na sauran jihohi da su yi koyi da Gwamna Makinde wajen hana hukumomi da cibiyoyin da lamarin ya shafa zabtare wani kaso daga kuɗaɗen maniyyatansu da suka rasa Hajjin 2022 suka kuma buƙaci a maida musu kuɗaɗensu.

Kafar ta ce wasu jijohin sun kai kuɗaɗen bankuna sun ɓoye don samun wani amfani amma duk da haka sai da suka ciri kaso daga kuɗaɗen maniyyatan.

IHR ta jaddada ƙudirinta na kare muradun maniyyata tare da kira ga jihohin da ke aikata ba daidai ba wajen taɓa kuɗaɗen maniyyata da su daina.