Cikin sanarwar da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun sakatarenta, Alh Umar Ahmed Chiroma, hukumar ta ayyana Naira miliyan 2.6 a matsayin mafi ƙarancin abin da maniyyaci a jihar zai biya a matsayin ajiya don tanadin zuwa Hajjin na bana.
Daga nan, Chiroma ya yi kira ga maniyyata Hajjin 2023 daga jihar su biya kuɗaɗensu cikin asusun hukumar a banki kafin 30 ga wannan wata da ake ciki.
Kazalika, ya shawarce su kan kada su biya kuɗaɗensu cikin asusun ɗaiɗaikun jama’a, yana mai gargaɗin hukumar ba za ta lamunci duk wani akasi da ya biyo baya ba sakamakon haka.
Ya ƙara da cewa, hukumar za ta sanar da al’umma da zarar aka samu ƙari ko ragi bayan Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), ta ba da sanarwa a hukumance kuɗin kujerar Hajjin 2023.