Kamfanin jirgin sama na Max Air ya sanar da naɗa Alhaji Abubakar Dahiru Mangal a matsayin sabon Babban Jami’in Zartarwa (CEO) na kamfanin.
Kamfanin ya naɗa sabon jami’in ne biyo bayan rasuwar Alhaji Bashir Mangal wanda Allah Ya yi wa rasuwa ran 23 ga Disamban bara.
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin, kamfanin ya ce sabon CEO ɗin na da ƙwarewar aiki na shekara bakwai inda ya riƙe muƙamin Mataimakin Daraktan sashen kuɗi na kamfanin.
Saƙon ya nuna, “Alhaji Abubakar yana da fahimta mai zurfi game da harkokin kamfanin.
“Muna da ƙwarin gwiwa a ƙarƙashinsa, kamfanin zai daɗa samun ɗaukaka da bunƙasa.”