Mata 255 sun shiga aikin jami’an tsaro na aikin Hajji a Saudiya

0
184

Karkashin jagorancin ministan harkokin cikin gida na kasar Saudiyya, Yarima Abdulaziz bin Saud bin Naif, Daraktan Tsaron Jama’a Laftanar Janar Muhammad Al-Bassami a ranar Laraba, ya halarci bikin yaye mata 255 na jami’an tsaro na musamman.

Sun kasance kashi na hudu na mata da aka dauka aiki, wadanda su ka kammala karatu a Makarantar horas da Sojoji ta da kwararru kan harkokin tsaro na Hajji da Umrah.

Za su shiga cikin runduna ta musamman mai kula da harkokin diflomasiyya da jami’an tsaron Hajji da Umrah.

Matan da su ka kammala karatun da ɗaukar horo sun sami horo kan aikace-aikacen da fasahar sadarwa, da kuma darussan akida da na aiki kan dabarun da ake bukata don gudanar da ayyukan tsaro.

Haka kuma sun samu horo kan tsari da tsarin aikin tsaro, baya ga shirya su kan wasu ayyuka na musamman da ake bukata domin gudanar da su daidai da yanayin aikinsu.

Saudiyya ta fara daukar mata da za su shiga sassa daban-daban na rundunar soji a shekarar 2019. An ba wa matan Saudiyya damar shiga aikin sojan Saudiyya, Royal Saudi Air Defence, Royal Saudi Navy, da na masarauta da Ma’aikatan lafiya na Sojan Saudiyya. , baya ga jami’an diflomasiyya, da jami’an tsaro na musamman na aikin Hajj da Umrah.