Hajjin bana: NAHCON ta gana da masu ruwa da tsaki a Madina

0
377

A ci gaba da shirye-shiryen Hajjin 2023 da take yi, Hukumar Hajji ta Najeriya (NAHCON), na ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki game da aikin Hajji a Saudiyya.

Tawagar hukumar ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Alh. Zikrullah Kunle Hassan, ta ziyarci kamfanin Adilla Establishments da Ma’aikatar Hajji da Umarah (reshen Madina) inda ta nuna godiyarta game da maido wa Najeriya kason kujerar Hajji 95,000 da ta saba samu a baya.

Yayin ziyarar, Hassan ya buƙaci a bai wa kashi 80 cikin 100 na maniyyatan Najeriya damar sauka da kuma ziyarar Madina kafin hawan Arfah.

Kazalika, ya roƙi a bai wa maniyyatan Najeriya damar zuwa Makka ƙarƙashin shirin nan na ‘Makkah Route Initiative’ ko kuma MRI a taƙaice.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Mataimakin Shugaban Adilla, Azmin Umar Abashi, ya yaba da ziyarar tawagar NAHCON, tare da alƙawarin za su taimaka wa hukumar ta kowace hanya da ta sawaƙa.

Kana ya nuna wa tawagar muhimmancin da ke akwai na bin ƙa’idoji da tsare-tsaren jigilar maniyyata.

An kuma tabbatar wa tawagar da cewa, za a dubi buƙatar da ta gabatar na saka maniyyatan Najeriya ƙarƙashin shirin MRI don cika mata burinta.

Yayin da suke Jidda, jami’i a Ofishin United Agents, Sahir Ibn Abdul Aziz Mootar, ya yi farin ciki da ziyarar tawagar NAHCON, inda a nan ma aka yi musu alƙawarin taimaka wa NAHCON ta kowace hanya don samun nasara yayin Hajjin bana.