Sama da maniyyata miliyan 2 ne za su yi aikin Hajjin 2023 – Saudiyya

0
377

Maniyyata sama da miliyan biyu ne, za su gudanar da aikin hajjin bana, in ji Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Kasar Saudiyya.

Ministan ma’aikatar, Dakta Tawfiq Al-Rabiah ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar.

Kafin s bullar annobar Korona a kasar, adadin alhazan da suka gudanar da aikin hajji sun kai yawan miliyan uku a 2012, inda ya nuna cewa, wannan ne adadin da yafi yawa a tarihin kasa.

A 2013, biyo bayan fadada aikin Babban Masallacin Harami, ya sanya mahukuntan Kasar Saudiyya, sun rage yawan maniyyatan da za su je kasar don yin aikin na hajjin.