Hajjin 2023: Za a fara jigilar maniyyatan bana ran 21 ga Mayu – GACA

0
156

Hukumar Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA), ta saki jadawalin yadda aikin jigilar maniyyata da alhazai zai kasance yayin Hajjin 2023.

Jadawalin da GACA ta fitar a yau Alhamis ya nuna cewa za a bude filin jirgin sama ga jirgi na farko aranar Lahadi, 21 ga Mayu, 2023.

GACA ta ƙara da cewa za a rufe filayen jirgin saman bayan dawowar jirgin karshe wajen kammala jigilar alhazan zuwa gida a ranar Alhamis, 22 ga Yunin 2023.

Yayin da jigilar alhazai da ga Saudiyya zuwa gida zai fara a ran Lahadi, 2 ga Yulin 2023, sannan a kammala ran Laraba, 2 ga Agusta.

Kazalika, GACA ta shawarci kasashen da za su yi Hajji da su miƙa bayanan da ake buƙata daga gare su kada ya wuce ranar Litinin, 29 ga Rajab wanda ya yi daidai da 20 ga Fabrairu, 2023.

Maniyyata sama da miliyan biyu ake sa ran za su yi Hajji bana a Masarautar Saudiyya.