Hajjin 2023: NAHCON ta sami sunayen kamfanunuwan da za su yi wa Nijeriya hidima a Saudiyya

0
366

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta fitar da jerin sunayen gidajen kwana da masu ba da abinci a kasar Saudiyya da aka amince da su don gudanar da aikin Hajjin bana.

Sunayen, wanda sashen yada labarai na hukumar ya rabawa manema labarai a jiya Alhamis ya nuna cewa, an zabo kamfanoni 42 ne domin samar da masauki ga maniyyatan Najeriya 95,000 da aka ware.

Haka kuma ya nuna an zabo kamfanoni saba’in da hudu da za su yi hidimar abinci ga maniyyatan.

Tun da farko dai hukumar NAHCON ta kulla yarjejeniya da Adillah Services wadanda ake sa ran za su gudanar da hidimar hidima ga alhazan Najeriya a Madina