Za mu gudanar da jigilar aikin Hajjin bana cikin nasara — NAHCON

0
214

Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON, ta bada tabbacin gudanar da aikin hajjin 2023 ga maniyyatan Najeriya cewa za a gudanar da shi lami-lafiya.

Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayar da wannan tabbacin ne a wata ziyarar da su ka kai a babban ofishin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta GACA da ke Jeddah a jiya Alhamis.

Ya nuna jin dadinsa da irin tallafin da Hukumar ta bayar a lokacin aikin Hajjin da ya gabata, inda ya kara jaddada aniyar NAHCON na ganin an samu nasarar gudanar da aikin hajjin 2023 ta hanyar sanya hannu kan yarjejeniyar farko ta aikin Hajjin bana.

“ina mai miƙa cikakkiyar godiyata ga hukumar bisa fahimta da goyon bayanta a aikin Hajjin shekarar da ta gabata, tare da tabbatar muku da cewa tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da wuri -wuri, za mu yi duk mai yiwuwa don ganin cewa an yi aikin Hajjin bana. Hajjin 2023 zai samu gagarumar nasara.

“A shirye mu ke mu yi hada-hadar aikin Hajji mai inganci da nasara.

“Hakika mun kuduri aniyar cimma hakan. Yanzu da mu ke da isasshen lokaci da dama don tsarawa da kuma tantance kamfanonin jiragen sama, ba za a sami damar yin korafi da uzuri ba, ”in ji shi.