Saudiyya da Ghana sun ƙulla yarjejeniya a kan aikin Hajjin bana

0
392

Mataimakin Ministan Hajji da Umrah na ƙasar Saudiyya, Dr Abdulfattah bin Suleiman Mashat, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da tawagar kasar Ghana da ke kasar Saudiyya, karkashin jagorancin Hajj Farouk Hamza, kan yadda za a gudanar da aikin hajjin bana, in ji wata sanarwa da ofishin jakadancin Saudiyya ya fitar a Accra, ta rahoton jaridar Ghana Times.

Wannan ya kasance wani ɓangare na taron hidimomin Hajji da Umrah da baje kolin (Hajj Expo 2023) da aka gudanar a Saudi Arabiya daga 9 zuwa ga watan Janairu.

Yarjejeniyar ta kasance wani bangare na shirye-shiryen farko da ma’aikatar ta yi na aikin Hajjin 2023 (1444H), da kuma kokarin saukaka zuwan maniyyata, da bunƙasa ingancin hidimar da ake yi musu da kuma inganta ibadar su da al’adunsu, a domin cimma muradun Hikimar 2030.

Yarjejeniyar dai ta haɗa da kason da aka ware, hanyoyin sauka da tashi, da kuma umarni na kungiya da ke inganta tsaro da jin dadin mahajjata, tun daga lokacin da ake shirye-shiryen tafiyar har zuwa barin kasar Saudiyya domin dawowa gida.